<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yesu Kristi Yana Zuwa Don Ya Ɗauki Masu Bi LW573</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Kristi yana zuwa don ya ɗauki masu bi
 Bar mu kasance da shiri, fitilinmu suna ci
 Wanda ya yi shiri duka zai tafi tare da shi
 Yesu yana dawowa a duniya.

[V2]
 KORUS
 Yesu yana dawowa a duniyan nan
 Don ya fyauci masu bi, Ya kai su can.
 Ka yi shiri fa mai bi, ka daidaita tafiyarka,
 Yesu yana dawowa a duniya.

[V3]
 2) Duba ango yana zuwa, ba labari, ba zato
 Ranan nan ba sauran tuba, ba kuwa wani taimako.
 Kada dai ka yi jinkiri har Ubangiji ya zo.
 Yesu yana dawowa a duniya.
 Korus

[V4]
 3) Wanda ba ya karɓi Yesu ba zai shiga damuwa,
 Babu sauran shirin kome, babu sauran gafara.
 Kai da ka ke ƙin Mai Ceto, rabonka sai balaka
 Yesu yana dawowa a duniya.
 Korus

[V5]
 4) Can a sama Gidan Allah, yawan daɗi za mu ji
 Muna nan tare da Yesu, muna hutawa da shi
 Babu sauran ɓacin zuciya, babu sauran a zunubi
 Yesu yana dawowa a duniya.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>573</hymn_number>
</song>